Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Basu Nasu, Mu Karbi Namu inji Madam Esther. Yakubu


Madam Esther Yakubu daya daga cikin iyayen 'yan matana makarantar Chibok da har yanzu Boko Haram na garkuwa dasu
Madam Esther Yakubu daya daga cikin iyayen 'yan matana makarantar Chibok da har yanzu Boko Haram na garkuwa dasu

Madam Esther Yakubu ta kira gwamnati ta biya bukatun kungiyar Boko Haram domin a sako masu 'ya'yansu wadanda sun kwashe fiye da shekaru biyu kungiyar Boko Haram na garkuwa dasu

Tayi kiran ne a tattaunawar da tayi da Muryar Amurka a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Tace bukatunsu ba masu wuya ba ne domin suna son a basu 'yanuwansu kana su ma su sako 'yan matan dake hannunsu.

Da aka tunasheta cewa sako 'yan Boko Haram din dake tsare ka iya yiwa kara yiwa tsaron kasar barazana sai tace ran mutun daya yafi wannan balantana ma rayukan mutane dari biyu da goma sha takwas.

Wasu cikin 'yan matan Chibok da har yanzu suna hannun kungiyar Boko Haram
Wasu cikin 'yan matan Chibok da har yanzu suna hannun kungiyar Boko Haram

A ganinta gwamnatin Najeriya taba da niyyar kwato 'yan matan. Abun da gwamnatin Buhari ta sa gaba shi ne habaka tattalin arzikin kasar.

Madam Yakubu tace ba'a damu dasu ba domin su talakawa ne. Idan da 'ya'yan masu hannu da shuni ne ko na manyan gwamnati da tuni an kwatosu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

XS
SM
MD
LG