Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Ghana kungiyar rajin kare zabe ta bukaci a sabunta rajistan zaben


Displaced youths from Daraa province clutch a barbed-wire fence on the Syria-Israel border near the Syrian village of al-Rafid during a demonstration against the regime, calling for international protection.
Displaced youths from Daraa province clutch a barbed-wire fence on the Syria-Israel border near the Syrian village of al-Rafid during a demonstration against the regime, calling for international protection.

Wata kungiyar matsin lamba da akewa lakabi da Let My Vote Count a Turance da ke rajin tabbatar da kuri’un jama’a sun yi tasiri a zabe, ta bukaci hukumar zaben kasar Ghana da ta kakkabe kundin rijistar sunayen masu zabe don amfani da shi a zaben Shugaban kasa da na Majalisa mai zuwa a watan Nuwambar bana.

Wannan kiran ya fito ne bayan kungiyar ta yi gangami tare da wasu kungiyoyin fararen hula dana ‘yan adawa a yankin ‘yan kabilar Ashanti da ke birnin Kumasi a jiya Laraba. Shugaban kungiyar David Asante yace, sun shirya yin zanga-zanga a fadin kasar don matsawa hukumar zaben tattaro sahihin kundin sunayen masu zaben.

Yace abin takaici ne ganin yadda hukumar bata yin amfani da rahoton kwamitin da ta kafa bata jin koken jama’a game da rashin sahihancin kundin sunayen masu zaben kasar da aka yi amfani da shi a zabeukan baya. Asante yace ba kuma wata maganar zama teburin yarjejeniyar janye wannan batu da suka faro.

Ya bayyana cewa, makasudin gangamin da za su gabatar a kasar shine, don tabbatar da cewa hukumar zaben kasar ta yi abinda ya kamata na ganin an aiwatar da sahihin zaben a zabukan kasar da ke tafe a watan 11 idan Allah ya kaimu. Saboda haka wannan na nuna cewa suna nan suna lura da al’amuran zabukan kasar.

XS
SM
MD
LG