Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A jihar Adamawa dubban yara na fama da cutar tamowa


Yara dake fama da tamowa
Yara dake fama da tamowa

Wani bincike da aka yi ya nuna yara fiye da dubu talatin da hudu ne suka kamu da cutar tamowa a jihar Adamawa saboda rashin shayar dasu da nonon uwa ba zalla na tsawon watanni shida.

Idan an cigaba da hakan adadin yaran da zasu dinga kamuwa da cutar tamowa zai dinga karuwa a jihar.

Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD tare da hadin gwuiwa gwamnatin jihar ta Adamawa sun shirya wani gangamin fadakar da kawunan iyaye mahimmancin shayarda yara nonon uwa.

Kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Dr Fatima Atiku Abubakar ta ba mata shawarar shayar da jariransu nonon uwa har na tsawon watanni shida. Tace nonon uwa na kunshe da sinadiran da jarirai ke bukata domin girma. Shan nonon uwa zai ba yaro daman samun kwakwalwar da ta dace da kuma yin girma yadda ya kamata.

Akan irin abuncin da iyaye zasu ci su ba jariransu nono kwamishaniyar tace dama mutanen Adamawa sun gaji noma. Abun da zasu yi shi ne su wayar da kawunan iyaye irin abincin da zasu noma da kuma zasu ci domin shayarda jariransu.

Kwamishaniyar ta kira 'yan jarida da su taimaka wurin wayar da kawunan iyaye akan mahimmancin ba jariri nonon uwa.

Wakiliyar asusun yara na MDD da wata jami'ar kiwon lafiya ta jihar Adamawa duk sun gargadi mata akan shayar da jariransu nononsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG