Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Mata Sun Shiga Takarar Zabe a Saudiya


A karon farkomata sun kada kuri'a sun kuma tsaya takara a Saudiya
A karon farkomata sun kada kuri'a sun kuma tsaya takara a Saudiya

Akalla mata 13 ne suka lashe zabuka a majalisun gundumomi da aka gudanar a kasar Saudiyya, wanda shi ne zabe na farko da aka baiwa mata dama su yi zabe su kuma tsaya takara a tarihin kasar.

Sakamakon farko ya nuna cewa, Salma Bint Hizab Al- Otiebi, ta zamanto mace ta farko da ta lashe zaben, inda ta doke maza bakwai da wasu mata biyu da suma suka tsaya neman kujerar Madrakah, gundmuar da ke da tazarar kilomita 150 da arewacin Makkah.

Shafukan yada labarai na gwamnati da saurarn kafafan yada labarai masu zaman kansu sun bayyana cewa akalla mata 17 ne suka yi nasara a wannan zabe, sai dai babu wani sakamako na karshe da aka fitar a hukumance.

Akalla mata 900 ne suka tsaya takarar neman mukamai dubu biyu, duk da irin kalubalan da suka fuskanta wajen neman takarar da kuma yin rajista, kamar yadda kungiyar Human Rights Watch mai kare hakkin bil adama ta bayyana.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta kara da cewa nisan rumfunan zabe da inda matan suke, da kuma rashin katin sheda da mafi yawan matan ba su dashi, na daga cikin ababan da suka janyo cikas wajen gudanar da zabukan.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG