Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Tun Bayan Sauka Daga Mulki Obama Ya Bayyana Ga Jama'a


Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya sake bayyana ga jama’a a jiya Litinin, inda ya yi kira ga matasa na garinsa Chicago da su kasance yan fafutuka a unguwanninsu kamar yanda ya yi kafin ya shiga siyasa.

A wani shirin hantsi da aka shirya a cikin harabar jami’ar Chicago, Obama ya fadawa taron jama’ar dake saurarensa cewar a lokacin da yake tattara jama’a, ya fahimci, idan talakawa suna aiki tare zasu iya yin abubuwa masu girma, wannan darasi ne da na dauka kuma yana tare da ni.


Shugaban Amurka na 44 shine ya jagoranci tawagar masu tattaunawar matasan da suka fito daga makarantun sakandare da jami’a da ma wadanda suka gama jami’ar suna ayyukansu, yace yana kyautata zaton zai taimaka da kuma shirya matasa da zasu ja ragamar duniya a wata rana.

Yace manyan kalubalai kamar na rashi daidaito wurin samun kudin shige, da na canjin yanayi da kuma rashin adalci a tsarin shari’a batutuwa ne na damuwa, sai dai ba zasu gagara magancewa ba.

Obama ya kama gabansa tun lokacin da ya kamala aikinsa a matsayin shugaban Amurka watanni uku da suka shige, inda ya yi watsi da irin dambarwan siyasa dake kunno kai Washington.

Obama dan jami’iyar Democrat ya caccaki wanda ya gajeshi hamshakin dan kasuwa mai gine-ginen gidaje Donald Trump a yakin neman zaben bara inda yace bai cancanci zama shugaban kasa ba, sai dai Obama yaki cewa uffan a salon mulkin Trump tun lokacin da ya dare shugaban Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG