Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Mali Sojojin Kasar Cadi Sun Fara Shiga Birnin Kidal


Sojojin kasar Mali
Sojojin kasar Mali
Sojojin daga Cadi sun fara shiga birnin Kidal, tungar karshe da ta rage hanun mayakan sakai masu ikirarin islama, kamin dakarun Faransa da Mali su kama birnin.

Yau talata jami’an Farans a suka ce kimanin sojojin Cadi dubu daya da dari takwas(1,800) sun fara shiga birnin. Wannan mataki yazo ne mako daya bayanda sojojin Mali da Faransa ta yiwa jagoranci, suka kama tashar saukar jiragen sama dake birnin.

Ma’aikatar tsaron Faransa ta fada cewa ta kai hare hare ta sama har 25 kan wasu muradun mayakan sakai masu ikirarin Musulunci cikin ‘yan kwanakin nan.

Faransa wacce ta kaddamar da shirin kutse a mali cikin watan jiya, ta bada sanarwar zata fara janye sojojinta sannu a hankali ta mika biranen da ta ‘yanto zuwa ga sojojin Mali da dakarun daga nahiyar Afirka.

Ranar litinin, jami’an Faransa suka bada sanarwar fara janye galibin sojojinta daga shahararren birnin nan na Timbuktu.

A wani cigaba, kungiyoyin kasa da kasa da jami’ai daga Mali suna taro talatan nan a binrin Brussels domin tattaunawa kan hanyoyin sake daidaita al’amura cikin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, data Afirka, da k,ungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka watau ECOWAS suna daga cikin wakilai kusan 45 da suke halartar taron.
XS
SM
MD
LG