Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Gwamnan Yamai Ya Sanar da Koran 'Yan Babbar Kasuwar Birnin


'Yan babbar kasuwar Yamai sun yi zanga zanga
'Yan babbar kasuwar Yamai sun yi zanga zanga

Korar 'yan kasuwa dake kewayen babbar kasuwar birnin Yamai da gwamnan Yamai din ya yi, ya haddasa zanga zanga da 'yan kasuwar suka gudanar na kin amincewa da matakin gwaman

Matakin da gwamnan Yamai Hamidu Garba ya dauka na korar 'yan kasuwa daga kewayen babbar kasuwar birnin ya gamu da fushin 'yan kasuwan.

A cikin takardar da ya aima kamsu ya basu nan da biyar ga watan gobe da su tara nasu -i-nasu, su fice daga inda suke kasuwanci abun da ya harzukar dasu suka fantsama yin zanga zanga.

'Yan kasuwar Yamai sun yi zanga zanga kan shirin tadasu daga babbar kasuwar birnin 7
'Yan kasuwar Yamai sun yi zanga zanga kan shirin tadasu daga babbar kasuwar birnin 7

Gwamnan ya zargi 'yan kasuwan da haddasa cunkoso lamarin da sautari ke kaiga hatsarin ababen hawa.

Saidai 'yan kasuwan sun ce rashin wurin zuwa ne ka sasu mamaye wuraren.

Wasu sun ce babu inda zasu domin su 'yan kasa ne. Suna da takardu na yin kasuwanci inda suke. Sun babu wata doka da zta iya korarsu.

Alhaji Sani Shekarau ya kira gwamnati ta su sassauta su samu yadda zasu warware matsalar cikin ruwan sanyi.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG