Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A nuna jinkai a batun 'yan gudun hijira dake kwarara zuwa turai - Davutoglu


Ahmet Davutoglu Firayim Ministan Turkiya
Ahmet Davutoglu Firayim Ministan Turkiya

Firai ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu, ya ce batun kwararar ‘yan gudun hijra a kasar, wadanda ke neman mafaka a nahiyar turai, ba batu ba ne da za a saka siyasa a ciki, batu ne da ya kamata a nuna jin kai ga bil adama.

Firai ministan ya bayyana hakan ne a yau Juma’a gabanin wani zama da ya yi da shugabannin kungiyar tarayyar turai a Brussels, domin cimma matsaya kan yadda za a mayar da dubun-dubatar bakin haure daga yankin turai zuwa Turkiyan.

A wani yunkurin na cimma matsaya kan batun bakin hauren da wasu masu rajin kare hakkin bil adama ke suka, ana sa ran kungiyar tarayyar turai ta yiwa Turkiya alkawarin samar da iznin yin zirga-zirga a yankin Schengen da kuma saka himma wajen bata damar shiga tarayyar ta turai.

Bangarorin biyu, sun cimma matsyar cewa akwai bukatar a dakile ayyukan masu fasa-kwaurin mutane, wadanda suke karban makudan kudade a hanun bakin hauren, domin su tsallaka da su zuwa Turkiyya da Girka da kuma Italiya a cikin yanayi mai cike da hadari.

XS
SM
MD
LG