Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Shekarar 2016 Mutane Miliyan 31.1 Suka Rasa Muhallansu Sanadiyar Tashin Hankali daBala'o'i -IDMC


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

Wata cibiyar gudanarda bincike ta kasa-da-kasa tace mutane milyan 31 da dubu 100 suka rasa muhallansu a shekarar da ta gabata ta 2016, duk a sanadin masifu iri-iri da suka hada da yake-yake, tashin hankulla da bala’o'i na halitta.

Cibiyar IDMC wacce bangare ce ta Hukumar ‘Yangudun Hijira ta kasar Norway ta NRC ce ta sako wadanan alkalumman a yau, inda tace a cikin shekarar ta 2016, anyi lokacinda bayan kowace dakika daya, akan samu mutum daya dake rasa mazauninsa a kasarsu.

Babban sakataren NRC, Jan (Yan) Egeland yace yanzu mutanen da suka rasa gidajensu sun fi ‘yan gudun hira yawa a duniya. Kiddidigar ta nuna cewa tashetanshen hankulla ne suka fi tada mutane tsaye, inda mutane kusan milyan bakwai suka rasa gidajensu, ciki harda a nahiyar Afrika inda mutane milyan 2 da dubu 600 suka rasa muhallansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG