Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Taraba Rikici Ya Sake Barkewa Tsakanin Makiyaya da Manoman Kabilar Kuteb


Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba
Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba na nuni da cewa wani sabon rikici ya sake barkewa a tsakanin yan kabilar Kuteb da kuma Fulani makiyaya a yankin Takum da Ussa dake kudancin jihar wanda kawo yanzu ba’a san adadin wadanda rikicin ya rutsa da su ba,koda yake tuni aka tura karin jami’an tsaro don shawo kan lamarin.

Kamar yadda rahotanni ke cewa ,yanzu wani sabon tashin hankali ne ya sake barkewa a tsakanin makiyaya da kuma kuteb tsakanin Takum da Ussa ,wanda kawo yanzu kuma ba’a tantance alkalumman rayukan da aka kashe ba.

Wannan sabon fadan na zuwa ne a kasa da sa'o'i 44 da kammala wani taron sasantawan da aka yi karkashin wata tawagar da gwamnatin jihar ta tura domin shiga tsakani ,kamar yadda wani dan yankin da bai son a ambaci sunansa ya shaida.

Da yake tabbatar da barkewa wannan sabon rikicin shugaban hadakar kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Sahabi Mahmud Tukur yace kawo yanzu akwai wasu makiyayan da ba’a san inda suke ba,baya ga shanun dake daji.

Gwamnan jihar Taraba,Akitet Darius Dickson Isiyaku ya nuna bacin ransa game da tashin hankalin inda ya danganta matsalar rashin hanya da cewa shike hana isa ga kauyukan da lamarin ke faruwa.

Gwamnan ta bakin hadiminsa ta fuskacin harkokin siyasa Abubakar Bawa ya bayyana matakan da ake dauka don gano bakin zaren magance tashin tashinan.

Kawo yanzu tuni aka tura jami’an tsaro don kwantar da rikicin,kamar yadda kakakin rundunan yan sandan jihar ASP David Misal ke cewa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG