Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Bam Ya Kashe Mutane 32 da Raunata Wasu 80 a Yola


Adamawa
Adamawa

Wani bam ya fashe a Yola babban birnin jihar Adamawa ya kashe mutane 32 tare da rauna wasu 80

Wadanda suka jikata suna kwance a sibitoci cikin garin Yola inda ake yi masu jinya.

Bam din ya tashi ne a wani waje dake da hada-hadar jama'a a tashar 'yan tipa a jambutu bye pass. Wurin bashi da nisa da Masallacin Juma'a inda makonni biyu da suka gabata wani bam ya tashi.

Alhaji Sa'adu Bello jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA ya bayyana halin da ake ciki yanzu.

Lamarin ya faru ne yayin da gwamnan jihar ke ziyarar aiki da shugaban kasa a jihar Kebbi.Batun ya tada hankalin gwamnan. Gwamnan ya yanke ziyarar aikin da ya keyi da shugaban kasa zai koma Yola yau.

Gwamnan yace zai sadu da jami'an tsaro su kara daukan matakai amma ya gargadi jama'a da su daina taruwa a wuri daya. Su dinga lura da duk inda suke. Ya kira a cigaba da yin addu'a.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG