Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubakar Shekau ya Dauki Alhakin Harin da Aka Kai Bama


Abubakar Shekau
Abubakar Shekau

A cikin wani bidyon da aka samu jumma’a, shugaban Boko Haram yace sune suka kai harin na ran 20 ga watan Disamba kan barikin soja.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, y ace sune suka kai hari kan wani barikin soja a yankin arewa maso gabashin kasar ranar 20 ga watan nan na Disamba.

Mayakan Boko Haram sun far ma barikin sojoji na garin Bama a Jihar Borno a cikin kwambar manyan motoci da daddare, suka bude wuta kan mutanen dake ciki, sannan suka cinna wuta. Shaidu da dama sun ce tsageran sun saci wasu sojoji da mata da yara suka tafi da su.

A cikin wani faifan bidiyon da ‘yan jarida suka samu Jumma’a, an ga Shekau zaune kan tabarma yayin da wasu ‘yan bindiga suke kewaye da shi, yana fadin cewa “mayakanmu sun abka cikin barikin Bama…Wannan nasara ce daga Allah.”

Shekau yayi ikirarin cewa sun lalata “tankoki 21” tare da kasha mutane masu yawa a wannan farmaki.

Rundunar sojojin Najeriya dai ta ce an kasha sojoji 15 a fadan da aka yi, yayin da ta ce ta kasha ‘yan ta’adda su 50. Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce ta kasha ‘yan ta’adda su fiye da hamsin a lokacin da sojoji tare da tallafin jiragen saman yaki suka bi sawun ‘yan Boko Haram dajke kokarin gudu bayan sun kai farmakin.

Mazauna garin na Bama da kuma kauyukan dake kusa sun fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an kasha fararen hula da dama yayin da aka lalata wasu kauyuka a martanin da sojoji suka maida.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG