Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abzinawa Masu Tawaye a Mali Sun Raba Gari da Abokan Yarjejeniyar Su


Abzinawan kasar Mali masu tawaye
Abzinawan kasar Mali masu tawaye

Yarjejeniyar neman kafa kasar Islama a arewacin kasar Mali ta ruguje

Abzinawa ‘yan tawayen kasar Mali sun janye daga yarjejeniyar da suka kulla da wata kungiya mai da’awar Islama a kasar da nufin hada kai su kafa kasa mai bin tafarkin Islama a arewacin Malin.

A cikin wata sanarwar da ‘yan tawayen suka gabatar ta imel a yau Jumma’a, daya daga cikin shugabannin su yace sun janye daga yarjejeniyar ce domin tabbatar da “cikakkiyar matsayar su da ba kunbiya-kunbiya a ciki’ ta neman tabbatar da raba harakar gwamnati da addini.

Yarjejeniyar da suka sanyawa hannu ranar 26 ga watan Mayu a garin Gao, ta bukaci Abzinawan 'yan tawaye da kungiyar Ansar Dine mai alaka da al-Qaida su hada karfi wajen kafa kasar Azawad mai cin gashin kai.

Kamar yadda yarjejeniyar ta yi tanadi sabuwar kasar zata bi tafarkin shari’ar Islama. A cikin makon nan rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar tana fuskanatar kalubale.

XS
SM
MD
LG