Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Yara, Mata Da Ke Mutuwa a Rikicin Afghanistan Na Karuwa - Rahoto


Wakilan Majalisar UNAMA Ta Majalisar Dinkin Duniya.
Wakilan Majalisar UNAMA Ta Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta sami rahoto mai ta da hankali na karuwar mace-macen mata da suka danganci rikici a Afghanistan da kashi 54, da kuma karuwar mace-macen kananan yara da kashi 17 a cikin watanni 4 na wannan shekarar ta 2017.

Idan aka kwatanta da mace-macen da aka samu a daidai wannan lokacin a shekarar da ta gabata.

Shirin ba da agajin na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan da ake kira UNAMA a takaice, wanda ya fitar da rahoton jimillar mace-macen yau Alhamis, ya ce akwai matukar damuwa akan karuwar mace-macen yara da mata.

Rahoton ya sami jimlar mace-macen fararen hula 715 a farkon shekarar nan, ciki har da mata 88 da yara 210.

Rikicin kuma ya jikkata fararen hula dubu daya da dari hudu da sittin da shida, ciki harda mata 185 da yara 525.

Shirin ba da agajin na UNAMA ya ce yara sune kashi 34 na mace-macen fararen hula da aka samu a cikin watanni 4 na wannan shekarar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG