Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Al'ummomin Birom da Filani Sun Yi Tur da Rikicin Filato


Tashin bom a Jos babban birnin Filato.
Tashin bom a Jos babban birnin Filato.

Al'ummomin Birom da Filani mazauna jihar Adamawa sun yi Allah wadai da rikicin dake yawan faruwa tsakanin mutanensu a jihar Filato.

Sun nuna rashin jin dadi da takaicinsu bisa ga irin hare-haren da Filani da Birom ke kaiwa juna a jihra Filato.

Haka kuma suka yi tur da wasu tashe-tashen hankula dake jihar ke fama dasu, musamman rikicin da ya sake barkewa kwana kwanan nan.

Sakamakon hakan ne suka yunkura wajen bada tasu gudummawar da zummar maido da zaman lafiya tsakanin al'ummomin biyu.

Shugaban al'ummar Birom na jihar Adamawa Yakubu Dawad da jami'in tuntubar jama'a na kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Adamawa Sanusi Bara sun ce bayan tuntubar juna da tattaunawar da suke yi loto-loto suna kuma ba mutanensu dake Filato shawarwari dangane da zaman lafiya da juna..

Bakin shugabannin ya zo daya. Kowannensu ya zargi jami'an tsaro da duna son rai da kuma rashin adalci a duk lokacin da aka samu barkewar rikici a jihar. Wannan lamarin sun ce yana dada ruruta rikici a jihar.

Rikicin Filato tsakanin Filani da Birom ya ki ci ya ki cinyewa. Ban da hakan rikicin na kawo cikas ga cigaban tattalin arziki da judanya da juna.

Shugaban Birom yace suna roko a rungumi zaman lafiya a jiharsu. Idan ba Fulani ba ne ke haddasa rikicin to ana bata masu suna. Su ma Filanin su yi bincike su san musabbabin rikicin. Daga ina bata garin suke fitowa.

Yayinda yake jawabi akan rikicin Sanusi Bara na kungiyar Filani yace a yi anfani da sakamakon binciken da gwamnatin Dariye ta yi. Akwai wasu baragurbi da suke shigo da Fulani daga kasar Mali saboda su hadasa rikici.

Ga karin bayani daga rahoton Sani Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG