Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Gidauniyar Tallafawa Jihohin Arewa Maso Gabas


Zaman Karbar Tallafin Bunkasa Asibitocin Michika Da Mubi
Zaman Karbar Tallafin Bunkasa Asibitocin Michika Da Mubi

Gidauniyar tallafawa jihohin arewa maso gabas da gwamnatin jihar Adamawa, sun saka hanu kan yarjejeniyar aiki kafada da kafada ta naira miliyan arba'in don sake gina asibitocin Michika da Mubi.

Da yake mikawa gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammad Umaru Jibirilla, takardar kudin a ofishinsa, babban daraktan gidauniyar wadda Janar T. Y Danjuma ke shugabanta, Farfesa Sunday Ochoche, ya ce an zabi asibitocin biyu ne bayan la'akari da gudunmawar da suka bayar wajen jinyar wadanda suka jikkata a hare-haren da Boko Haram suka rika kaiwa mazauna yankin.

Baya ga gyaran asibitocin, akwai manyan ayyukan da gidauniyar za ta aiwatar da suka hada da sake gina sakatariyar ta karamar hukumar Michika da kuma gina makarantu bakwai a kananan hukumomin Mubi da Hong. Farfesa Ochoche, ya ce bara gidauniyar ta tallafawa dalibai dubu goma sha biyu da kayayyakin da suka bukata don karatu.

Akwai matakai da sharudan da gidauniyar ta shimfida na aiwatar da ayyukan ta da kudin da take baiwa jihohi gudumawa don gudun Kada su karkatar su ta wata hanya inji Farfesa Sunday Ochoche, lokacin da ya ke amsa tambayar ko ba su ganin in ba an yi taka sansan ba gwamnatocin jihohin ba za suke yin anfani da kudin nan ta hanyar da ta dace ba.

Gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Umaru Jibrilla, ya ce za a dauki lokacin mai tsawo ana gyara, saboda barnar da yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka aikata, don haka jiharsa ke ci gaba da neman Karin tallafi na samar da muhimman kayan rayuwa.

A kananan hukumomin Gombi da Maiha, gidauniyar ta zabi marayu dubu ‘daya wadanda ta dankawa wasu iyaye amanar kulawa da rayuwa da ilimantar da su ta hanyar baiwa kowanne iyali tallafin naira dubu goma sha hudu kowace wata.

Daya data cikin iyayen Mallam Abba Mohammed, a karamar hukumar Maiha ya ce wannan tallafin zai taimaka wajen renan shugabanni na gari daga cikin marayun nan gaba.

Saurari rahoton Sanusi Adamu domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG