Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai fargabar tashin hankali a Janhuriyar Kongo-Kinshasa, an jinkirta sanar da sakamakon zabe


Shugaban Kongo Joseph Kabila na kada kuri'a
Shugaban Kongo Joseph Kabila na kada kuri'a

Kafofin yada labaran gwamnati a janhuriyar demokaradiyyar Kongo,

Kafofin yada labaran gwamnati a janhuriyar demokaradiyyar Kongo, sun ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar za ta jinkirta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na tsawon sa’o’i 48.

Hukumar ta fadi da yammacin jiya Talata cewa ta na bukatar karin lokaci, don harhada sakamakon daga sassan wannan kasa ta yankin tsakiyar Afirka, sannan ta yi alkawarin bayar da cikakken sakamako zuwa ranar Alhamis.

Jinkirta sanar da cikakken sakamakon wuccin gadin zai dada cusa tsoro a wannan al’marin siyasa, wanda tuni ma ya ke ta kara tabarbarewa. Jami’an zaben sun so su sanar da wanda ya ci zaben kafin karewar wa’adin shugaba Joseph Kabila da tsakad daren jiya Talata.

Dubban sojoji na sintiri bisa tituna a Kinshasa, babban birnin kasar, da wasu kuma sauran birane saboda tarar yiwuwar zanga-zanga.

Ofishin Jakadancin Amurka ya umurci ma’aikatansa cewa kar su fice daga unguwar Gombe, saboda rashin sanin tabbas game da yanayin tsaro.

Jami’an zaben sun ce ganin yadda aka riga aka kidaya 2/3 na kuri’un, shugaban Kabila ya sha gaban babban mai kalubalantarsa Etienne Tshisekedi, da kuri’u kashi 46% akasin kashi 36%.

Bangarorin biyu dai kowannensu ya nuna alamar za a yi tashin hankali, muddun ba shi ya yi nasara ba.

Gwamnati ta tura jirage masu saukar ungulu zuwa wurare masu wuyar zuwa, don dauko alkwatunan zabe.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG