Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alamu Guda Biyar Na Cutar Shanyewar Sashin Jiki


Wani mutum mai fama da cutar shanyewar sashin jiki
Wani mutum mai fama da cutar shanyewar sashin jiki

Mutuwar jiki ko nauyin jiki musamman ma a gefe guda na iya faruwa a fuska, kafada, ko kuma kafa.

Mutuwar jiki ko nauyin jiki musamman ma a gefe guda na iya faruwa a fuska, kafada, ko kuma kafa. Kungiyar kula da shanyewar sashin jiki na kasa sun bada shawarar cewa idan wanda kake tare da shi ya nuna wata alama kamar haka, kace wa mutumin yayi murmushi, ya daga dukan hannuwansa tare, ko ya motsa kafafunsa. Inji kungiyar shanyewan sashin jiki na kasa, idan wani sashi na jikin bai iya yi kamar sauran ba, zai iya yiwuwa cutar shanyewar sashin jiki ce.

1. Rikicewa ko kasa magan: Idan mutumin na samun wahala wajen yin magana ko fahimta, abinda ake kira aphasia, zai iya zama cewa jini baya zuwa wannan sashi na kwakwalwa wanda ke lura da harshe. Ka sa mutumin ya maimaita wata magana ta layi daya. Idan yana jan baki ko kuma maganar bata fita, wannan na iya zama alamar matsala.

2. Wahalar gani da tunani: Shanyewra sashi jiki na iya rage kaifin gani na ido daya ko dukan idanuwa ko kuma ya sa a riga ganin abubuwa biyu biyu. Zai kuma iya kawo wa mutum rashin iya gane wasu abubuwa ko mutane, ko kuma matsalar banbanta abinda ya gani na ido ko na madubi.

3. Wahalar motsawa: Rashin iya tsayawa daidai (jin jiri) da kasa tafiya, wannan ya nuna cewa sashin kwakwalwar dake kula da jijiyoyin jikin ya sami matsala.

4. Ciwon kai mai zafi: Ciwon kai mai zafi mara dalili shima alamar shanyewar sashin jiki ne, yawanci irin wannan ya kan sami dangantaka da fashewar jijiyar jini a kai.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG