Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalin wata babbar kotun Amurka ya yankewa wani dan Mali hukumcin shekaru 25


Antoni Janar ta Amurka Loretta Lynch
Antoni Janar ta Amurka Loretta Lynch

Alkalin wata babbar kotun Amurka, ya yankewa wani dan kasar Mali, mai alaka da masu tsatstsauran ra'ayi- hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari, saboda kisan wani jami'in difilomasiyyar Amurka, shekaru 15 da suka wuce a Nijar.

A shekara ta 2013 aka kama kuma aka tuhumi Alhassane Ould Mohammed, kan zargin kisan William Bultemeier, da kuma yunkurin kashe wani sojan Amurka, yayinda mutanen biyu suke barin wani wurin cin abinci a birnin Niamey, babban birnin kasar Nijar a shekara ta 2000.

Masu bincike suka ce Mohammed, mai inkiya Cheibani, da wani mutum sun tunkari Amurkawan biyu, suka nemi su basu makullin motarsu, mai lasin difilomasiyyar Amurka. Masu gabatar da kara suka ce mutanen biyu suka bude wuta kan Amurkawan, suka kashe Bulteimer, suka kuma raunata sojan-saje Christopher MCneely.

Bayan da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a Mali kan wannan laifi, sai ya tsere daga gidan fursina.

A 2013 ne dakarun faransa suka kama shi daga bisani suka mikashi ga Amurka.

Ahalinda ake ciki kuma,an kashe mutane 11, ciki harda sojoji takwas a wani barikin soja a Cape Verde.

Jami'ai a kasar dake a Afirka ta yamma suka ce, wani soja da ya bijire kuma yayi layar zana ne, ya kashe sojojin da fararen hula uku, ciki harda 'yan kasar Spain biyu.

Wata sanarwa da hukumomin kasar suka wallafa a shafinsu na internet sun danganta lamarin ga wani sabani ko dalili wanda bashi da nasaba da yunkurin juyin mulki, ko tarzoma da ake dangantawa da miyagun kwayoyi ba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG