Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Yiwa Sanata Dahiru Kuta Rasuwa


Marigayi Senator Dahiru Awaisu Kuta mai wakiltar gabashin jihar Neja a majalisar dattawan Najeriya.
Marigayi Senator Dahiru Awaisu Kuta mai wakiltar gabashin jihar Neja a majalisar dattawan Najeriya.

Jiya Alhamis Allah Ya yiwa Sanata Dahiru Awaisu Kuta rasuwa a wani asibiti a Legas

Masarautar Minna ta sanarda rasuwar Sanata Dahiru Awaisu Kuta.

Sanatan ya rasu jiya da sanyin safiya a wani asibiti a Legas. Kafin rasuwarsa ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Neja a shekarar 1983. Hakazalika an taba zabansa ya zama dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya a shekarar 1993. Daga bisani ya zama mataimakin darakta na jam'iyyar PDP na kasa.

Da ya koma jihar Neja ya zama sakataren gwamnatin jihar Neja a lokacin da Injiniya Abdulkadiri Kure ke gwamnan jihar. A cikin watan Afrilun 2007 ne dai aka zabeshi ya zama dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar gabashin jihar Neja.

A bangaren ilimi kuwa Sanata Dahiru Kuta yayi digirinsa na farko a Jami'ar Bayero dake Kano. Yayi kuma digiri na biyu a Jami'ar Ile-Ife.

Sanatan ya rasu ya bar mata daya da yara guda hudu. Za'a yi jana'izarsa a babban masalacin Jumma'a dake birnin Minna fadar gwamnatin jihar Neja.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:55 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG