Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummomi a Najeriya sun kai karar gwamnati kan batun rusa gidaje


Wadansu kauyuka a birnin tarayya sun kai karar gwamnatin tarayya

Kauyuka goma sha tara dake babban birnin tarayyar Najeriya sun kai karar gwamnati suna nema a dakatar da shirin rusa masu gidaje da kuma wuraren kasuwancinsu.

Gwamnatin tarayyar Najeriya tana shirin rusa wadansu matsugunai ne a karshen wannan watan a unguwar Mpape da kuma wadansu matsugunai goma sha takwas take babban birnin tarayya, da mazauna wurin suke kira “Villages”

Mazauna wurin sun bayyana cewa, idan aka rusa gidajen zasu rasa wurin da zasu sa kansu. ‘Yan gwaggwarmaya sun bayyana cewa, kimanin mutanen miliyan daya da dubu dari takwas zasu rasa muhalli idan aka rusa gidajen, sai dai hukumomi sun karyata adadin.

Gwamnati tace kusan dukan wadanda suke zaune a yankin ‘yan share wuri zauna ne, kuma basu musanta haka ba. Da dama daga cikinsu sun ce sun sayi filayen ne daga hannun wadanda suke zaune a wurin da, amma basu da takardun shaidar mallakar filaye daga gwamnati.

An maida Abuja babban birnin tarayya ne a shekara ta dubu da dari tara da saba’in a da nufin hada kan kasa bayan yakin basasa da ya daidaita kasar. Birnin na cike da manyan gidaje masu kawa da gine ginen gwamnati da kuma filaye da wuraren shakatawa da aka kawata.

Lauyan da yake kare al’ummomin, Wahab Olatoye, ya zargi jami’an gwamnati da amfani da tsarin birnin a matsayin hujjar kwace filayen daga talakawa, su ba attajirai.

Yayinda birnin Abuja ke habaka, ‘yan Najeriya masu karamin karfi, wadanda akasarinsu suke fama da mummunan talauci, da rashin wurin kwana mai kyau, ko kula da lafiyarsu, suna kara shiga matsugunai marasa kyau kamar Mpape inda babu ruwan sha mai tsabta, babu wutar lantarki ba kuma hanyoyi.

XS
SM
MD
LG