Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aminu Waziri Tambuwal Ne Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ta Tarayya


Tsoffin shugabannin Najeriya a bikin rantsar da shugaban Najeriya a Abuja
Tsoffin shugabannin Najeriya a bikin rantsar da shugaban Najeriya a Abuja

Duk da an kai gwauro aka kai mari,kan neman tilastawa wakilai a majalisar wakilai ta tarayya wajen zaben kakakin majalisa kan tsarin karba karba yaci tura.

Kamin ayi zaben sabon kakakin majalisar wakilai a majalisar wakilai ta tarayya, ta bakwai a Abuja, sai da jiga jigan PDP da suka hada da mukaddashin shugaban Jam'iyya ta kasa, Dr. Bello Halliru,da daya daga cikin wakilan kwamitin amintattun jam'iyyar Mr. Anenih, suka sake ganawa da wakilan majalisar wakilai 'yan Jam'iyyar PDP, domin tuna musu burin jam'iyyar na ganin an mutunta tsarin karba-karba.

Ganin yadda zabe ya kaya,Jam'iyyar bata sami biyan bukata ba. Wakilai 252 suka zabi Aminu Waziri Tambuwal,yayinda abokiyar takararsa, Malama Mulikatu Akande Adeola, ta sami kuri'u 90. Anyi watsi da kuri'u takwas, mutum daya baya nan,cikin wakilai 362.

Bayan rantsuwar kama aiki,sabon kakakin majalisar wakilai Aminu Tambuwal,yayi alkawarin bude sabon babi a gudanar da harkokin majalisa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG