Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Zata Tura Tawaga Zuwa Taron Sulhu Kan Rikicin Syria Ba.


Baraguzan motar da aka nasawa Bam a sansanin 'yan gudun hijira a Jordan.
Baraguzan motar da aka nasawa Bam a sansanin 'yan gudun hijira a Jordan.

Duk da haka ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace zata tura dan kallo jakadanta dake Kazakhs.

Jiya Asabar, Amurka ta bayyana cewa ba zata tura tawaga zuwa taron share fage na neman sasanta rikicin siyasar Syria, wadda za'a fara cikin makon nan a Astana, babban birnin kasar kazakhstan, maimakon haka tace zata tura dan kallo.

Saboda dalilai na shirye shiryen karbar mulki, ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace, jakadan Amurka a Kazakhstan George Kroll ,zai halarci taron da kawar Syria-Rasha, tareda Turkiyya da Iran suka shirya, ba tareda yawun Amurka ba.

Gwamnatin Syria ta shugaba Assad, tace a shirye take a gudanar da shawarwari "kan ko wani batu" a lokacin taron da za'a fara gobe Litinin, sai dai wasu kungiyoyin 'yan tawayen kasar suka ce zasu fi maida hankali ne wajen tabbatar da ana mutunta yarjeniyar tsagaita wutar da take aiki yanzu a kasar.

Haka nan 'yan tawaye suka ce ba zasu yi shawarwari kan warware rikicin kasar a ahalin yanzu ba.

Wata kungiyar 'yan tawaye mai alaka da al-Qaida Fatah al-sham wacce bata cikin kungiyoyi d a zasu halarci taron sulhun ba ta kira zaman a zaman wata makarkashiya.

A farkon makon jiya Fatah- al-sham ta farwa wata kungiyar 'yan tawaye da ake kira Ahrar al-sham a lardin Idlib. fatah ta kai mata harin bayan shawarwarin d a kungiyoyin biyu suka yi na shirin hadewa ya wargaje.

A wasu labarai kungiyar kare hakkin Bil'Adama ta Syria, tace wani bam da aka nas a cikin mota ya tashi a wani sansanin 'yan gudun hijira a kusa da kan iyakar kasar da Jordan, mutane shida ne suka halaka, wasu fiyeda 20 kuma suka jikkta.

XS
SM
MD
LG