Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da kawayenta sai sun ga bayan kungiyar ISIS - Obama


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, rundunar sojojin taron dangin da Amurka ke jagoranta na da manufar yaki da ta’addancin ISIS, sannan rundunar ta yi duk wani tsarin da ya kamata don tsayawa akan wannan kuduri nata na kakkabe ‘yan ta’addan.

Obama yace, “a yau a kasheshen Syria da Iraki, yan ISIS sun koma yakin kare kansu ne kawai, saboda ratattakar da tawagar sojojin kasashe 66 hade dana Larabawa ke musu ta sama da kasa. Inda shugaban yace a karkashin jagorancin Amurkan an kai harin rokoki ta sama fiye da sau Dubu 11 da 500 da ya hallaka mayakan da dama.

Ya kara da cewa, a kullum mayakan ISIS da ke Syria da Irakin sai karewa suke yi, wanda aka kiyasta cewa lallai sojojin sa kan ta’addancin sun kai matakin karshen na rashin yawa idan aka yi la’akari da yawansu a shekaru biyu da suka wuce.

Sannan da yawan mayakan sun lura da cewa kullum suna kara nisanta daga samun nasara akan mayakan taron dangin, inji Obama. Ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da tawagar tsaro a shelkwatar jami’an tsaron leken asiri ta CIA da ke jihar Viginia ta nan Amurka, kamar yadda ya fada a taron cibiyar tsaro ta Pentagon.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG