Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Norway zasu hada hannu wajen inganta lafiyar mata a Afrika.


Sakatariyar harkokin wajen Amurka,Hillary Clinton
Sakatariyar harkokin wajen Amurka,Hillary Clinton

Kasar Amurka da kuma Norway zasu hada hannu wajen inganta lafiyar mata da kananan yara a nahiyar Afrika.

Kasar Amurka da kuma Norway zasu hada hannu wajen inganta lafiyar mata da kananan yara a nahiyar Afrika.

Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyana cewa, za a gudanar da shirin da aka ba lakabi “Saving Mothers, Giving Life”, da nufin rage mace- macen mata da kananan yara, a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya tace mata 800 suke mutuwa kowacce rana a wajen haihuwa.

Za’a a aiwatar da shirin na hadin guiwa tsakanin Amurka da kasar Norway ne tare da hadin kan wani kamfanin harhada magunguna Merck da kuma kungiyar likitocin kula da lafiyar mata ta Amurka.

Shirin da za a fara aiwatarwa a kasashen Uganda da Zambia, zai bada karfi kan taimakawa mata a lokacin da suka je haihuwa da kuma bayan sa’oi 24 da haihuwa, lokacin da ake asarar kimanin mata biyu a cikin uku dake rasa rayukansu lokacin haihuwa.

Za a gudanar da shirin na hadin guiwa tsakanin gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu da nufin inganta ayyukan jinya a yankunan ta wajen gina dakunan magani da dakunan binciken kwakwa, da horas da ma’aikata da inganta hanyar samar da jinni da kuma tsarin ajiye bayanan jinya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG