Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Saudiya sun amince da yin aiki domin kawar da rikicin yankin Gulf


Shugaban Amurka Obama da Sarkin Saudiya Salman
Shugaban Amurka Obama da Sarkin Saudiya Salman

Shugaban Amurka Barack Obama da Sarki Salman na Saudiyya, sun amince da muhimmancin yin aiki tukuru don kauda rikicin da yankin yake fuskanta. Sun aiwatar da haka ne a wata ganawar sirri ta sa’o’i 2 a birnin Riyadh babban birnin Saudi.

A wata sanarwar da aka fidda bayan taron a Fadar Erga a can kasar, fadar White House tace, shugabannin sun tattauna kalubalen da Iran ke haifarwa yankin gabas ta tsakiya bisa takalar fada.

Amurka da Saudiyya sun lura da samun karuwar fargaba bisa yadda Iran din ke fuskantar al’amuran yaki da ‘yan ta’adda a yankin. Sanarwa tace Obama ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar rikicin Yamal, da kuma kokarin Sarkin Saudiyyar game ta kai kayan agaji a kasar.

Shugaba Obama ya sake jaddada muhimmancin sake aza kaimi wajen yakar ‘yan ta’addar ISIS, sannan ya yaba da rawar da Saudi ke takawa a cikin hadakar sojojin taron dangin da take jagoranta. Daga baya Obama ya gana da Yarima Sheikh Mohammed bin Zayed al- Nahyan na Abu Dhabi da Mataimakin babban kwamandan rudunar Sojojin hadaddiyar daular Larabawa.

XS
SM
MD
LG