Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho jiya Litinin, mukaddashin sakataren ma'aikatar Alejandro Mayorkas, yace yana da kwarin guiwa zasu tabbatarwa gwamnonin cewa babu wani dalili na fargaba.
Gwamnonin wasu jihohi fiyeda 24 ne suka ayyana turjiya na karbar 'yan gudun hijira daga Syria a jihohin nasu, bayan da aka gano cewa daya daga cikin mutanen da suka kai hari a Paris, dan ta'adda ne da ya saci-jiki yabi 'yan gudun hijira da suke gudu daga yakin basasar kasar Syria ya shiga Turai.
Gwamnonin sun nemi da a kawo karshen shirin sake tsugunarda 'yan gudun hijira kimanin dubu 10 daga Syria anan Amurka badi,a muhawara da ake yi anan Amurka, shigen wadanda ake yi a kasashen Turai cewa karbar ‘yan gudun hijiran yana jefa tsaron kasashen cikin hadari.