Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Jami'an tsaro sun cafke wasu 'yan gudun hijira biyu daga Iraqi


Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Shari'ar Amurka Loretta Lynch
Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Shari'ar Amurka Loretta Lynch

Yayin da wasu gwamnonin Amurka ke kushewa shigo da 'yan gudun hijira daga kasashen gabas ta tsakiya sai gashi mahukunta sun cafke 'yan gudun hijira biyu 'yan asalin kasar Iraqi kan zargin shirin aikata ta'adanci.

Jami'an gwamnatin tarayyar Amurka sun cafke mutane biyu 'yan gudun hijira daga kasar Iraqi akan laifin da ya jibanci ta'adanci.

Lamarin ya sa amurkawa na kara sukan shirin gwamnatin kasar na tsugunar da wasu sabbin 'yan gudun hijira daga gabas ta tsakiya.

Mutanen da aka cafke falasdinawa ne daga kasar Iraqi kuma sun dade suna zaune cikin Amurka. Ana kyautata zaton mutanen suna da alaka da juna kodayake babu alamar suna shirin aikata ta'adanci tare kamar yadda wani jami'in gwamnati ya fada.

Bayanai daga ma'aikatar harkokin shari'ar Amurka sun nuna cewa Aws Mohammed Younis Al-Jayab dan shekara 23 da haihuwa an cafkeshi ne ranar Alhamis a Sacramento dake jihar California inda ake zarginsa da yin karya kan abun da ya shafi ta'adanci a kasa da kasa.

Shi Al-Jayab ya shigo Amurka ne a shekarar 2012 daga Syria a matsayin dan gudun hijira. Ana zarginsa da shata karya akan tafi-tafiyensa zuwa Syria inda aka ce ya yi yaki da dakarun kungiyar Ansar al-Islam mai tsananin ra'ayin addini.

Omar Faraj Saeed Al-Hardan dan shekara 24 an cafkeshi ne a Houston dake jihar Texas. Shi kuma ana zarginsa ne da kokarin baiwa kungiyar ISIS goyon baya da abubuwan da suka hada da horo da shawarwari irin na kwararru.

Shi ma Al-Hardan ya shiga Amurka ne a matsayin dan gudun hijira daga Iraqi a shekarar 2009 kafin daga baya ya sami katin zama kasar na din-din-din. Shi ana zarginsa da shata karya yayinda yake neman zama dan kasa dangane da dangantakarsa da kungiyoyin 'yan ta'ada.

Yau ake zaton za'a gurfanar da mutanen biyu gaban shari'a.

Tuhumar da ake yiwa wadannan mutanen biyu ka iya zafafa muhawara cikin Amurka akan shirin Fadar White House na cigaba da karbar 'yan gudun hijira dubu goma daga Syria duk da shakkun da ake dashi akan tsaro.

A jihar Texas inda gwamnati ta yi kokarin hana tsugunar da 'yan gudun hijira daga Syria. Gwamnan jihar Greg Abbott yayi anfani da kamun ya kara sukar manufar gwamnatin tarayya kan kara shigo da 'yan gudun hijira.

XS
SM
MD
LG