Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Jagorantar Wani Atisayen Soja a Ruwan Najeriya


A yau ne mayakan ruwa daga kasashe duniya 30 suka fara wani atisaye na shekara- shekara akan tekun Najeriya.

Atisayen mai taken "Obangame Express" rundunar mayakan Amurka, dake Afirka ta “US Afri Commad” ke daukar nauyinsa

Baya ga kasashen Afirka, akwai wasu kasashen dake wajen nahiyar Afirka kamar su Belgium, Brazil Denmark, Norway, Turkey da Netherlands, dake halartar atisayen.

Ko a baya an gudanar da irin wannan atisayen a Najeriya, hakan kuma ya karfafa hadin kai da ma’amala da yarda tsakanin dakarun ruwan kasashen Afirka maso kudu da maso yamma kuma ya taimaka wajen magance wasu matsalolin dake addabar ruwan yankin in ji Navy Captain Suleman Dahun dake wakiltar Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG