Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Neman Hanyar Kawo Karshen Barazanar Koriya Ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci shawarar jami'ai, kan yadda zai kawo karshen barazanar nukiliya daga Koriya Ta Arewa. Mai ba Kasa Shawara kan Tsaro Herbert Raymond McMaster ne ya fada jiya Lahadi.

Yayin da sojojin ruwa na Amurka su ka danna zuwa yankin ruwayen Koriya a matsayin gargadi ga Koriya Ta Arewa, McMaster ya gaya ma kafar labarai ta FOX Newa cewa, "Gwamnati ce marar natsuwa, wadda a yanzu kuma ta zama mai iya yin makaman nukiliya ... Saboda haka Shugaban kasa ya gaya ma na cewa mu kasance a shirye saboda za mu gabatar masa da jerin zabi na kawar da wannan barazanar da mutanen Amurka da abokanmu da kuma da kuma masu alaka da mu a yakin."

McMaster ya bayyana shawarar da Amurka ta yanke ta tura bataliyar Carl Vinson don ta kare muradun Amurka a yankin na Yammacin Pacific da "abin da ya dace." Ya ce Trump da Shugaban China Xi Jinping sun amince a ganawarsu ta makon jiya a Florida cewa takalar da Koriya Ta Arewa ta ke yi ta wajen kirkiro makamin nuliliya ba za a lamunta da shi ita ba.

"Shugabannin da su ka gabata da kuma Shugaba Trump duk sun amince cewa abu ne da ba za a lamunta da shi ba, don haka abin da ya kasance wajibi shi ne a kawar da nukiliya daga wannan yankin ruwayen," a cewar McMaster.

Koriya Ta Arewa dai ta yi ta kokarin kirkiro makamin nukiliya wanda zai iya isa Amurka, wato tazarar kilomita 8,000. Ya zuwa yanzu dai ta kaddamar da gwaje-gwajen nukiliya har biyar kuma mai yiwuwa ta na kan shirin na shida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG