Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Tuhumar Julian Assange


Shugaban Wikileaks Julian Assange
Shugaban Wikileaks Julian Assange

Wata majiya a Amurka ta fadawa kafar yada labarai ta CNN cewar gwamnatin Amurka na shirin  tuhumar Julian Assange dan kasar Austaralia nan wanda ya shahara saboda shafinsa na kwarmata bayanan sirri da ake kira Wikileaks.

Tun shekarar 2010 Ma’aikatar shari’ar Amurka take gudanar da binciken kan Assange, bayan da Wikileaks ta buga dubban takardun sirri da aka sace na Amurka, wadanda ke da alaka da lamarin tsaro.

A cikin makon jiya ne, shugaban hukumar CIA ta leken asiri na Amurka, Mike Pompeo ya fada a wani jawabi da ya yi a Washington DC cewa, Wikileaks ta umarci wani jami’an tsaron Amurka soji da ya tono wasu bayanai na musanman da suka shafi Amurka.

Jaridar Washington Post ta ba da rahoton cewa lauyoyin ma’aikatar shari’ar Amurka na ta shirya kararrakin da suka shafi irin hukuncin da za’a yanke wa mutanen da ke da alaka da Wikileaks.

Amma jaridar ta ce rahoton kowanne hukunci akan wadannan mutane na bukatar izini daga wajen manyan ma’aikatan shari’a .

Jami’an leken asirin Amurka sun ce Rasha ta yi amfani da Wikileaks domin buga sakonnin email na tsohuwar 'yar takarar shugabancin kasar Amurka Hillary Clinton a zaben shekarar da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG