Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin yin Atisayen Jiragen Ruwan Yaki a tekun Bahar Asfar


Sojojin Ruwa Bisa George Washington.
Sojojin Ruwa Bisa George Washington.

Amurka da Koriya ta Kudu za su yi Atisayen Hadin Gwiwa a tekun Bahar Asfar a farkon watan gobe.

Amurka ta ce za ta yi atisayen soji na hadin gwiwa da Koriya ta Kudu a Tekun Bahar Asfar a farkon Watan gobe. Mai magana da yawun Hedikwatan Tsaron Amurka Pentagon, Bryan Whitman, ya fadi yau Laraba cewa atisayen zai fi bayar da karfi ne ga kare kai daga harin jiragen yakin karkashin ruwa. Bai bayyana irin jiragen ruwan da za a yi amfani da su ba, amman y ace ba irin atisayen da yawancin lokaci akan yi amfani da katafaren jirgin ruwan daukan jiragen yakin nan mai suna USS George Washington.

Shi dai jirgin George Washington ya taka muhimmiyar rawa a atisayen Amurka da Koriya ta Kudu a watan jiya wanda aka kawar da shi daga Bahar Asfar zuwa Tekun Japan bayan da China ta nuna kin amincewarta.

Amurka ta ce jirgin George Washington zai shiga atisayen jiragen ruwan yakin da za a yi a karshen wannan shekarar. China ta yi gargadi makon jiya cewa tura jirgin daukar jiragen yakin zuwa sashen tekun da ke tsakanin ita Chinar da Koriya ta Kudu zai zama takalar fada da kuma barazana ga tsaronta.

Whitman y ace atisayen na Satumba za a yi ne saboda Koriya ta Arewa kuma ba zai yi wata baraza ga tsaron China ba.

XS
SM
MD
LG