Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Yunkurin Shigo Da Karin Masu Gudun Hijirar Syria


Ana Saura kimanin makwanni biyu shekarar kudi ta zo karshe, kungiyoyi masu tallafawa yan gudun hijira a nan Amurka suna cikin tsakiyar abin da ake kyautata zaton zai zama kwararrar baki mafi girma a cikin sama da shekaru goma, biyo bayan yunkurin shigo da Karin masu gudun hijira da yakin basasa a Syria da IS ta raba da muhallansu.

Ya zuwa ranar 15 ga watan Satumba kimanin yan gudun hijira dubu 79 daga kasashe 78 ne suka shigo Amurka tun watan Oktoba. Adadin da yafi wanda aka samu cikin shekaru 17, inji wani jam’in bayanai.
Shirin yan gudun hijira na Amurka da ma’aikatun gwamnati ke gudanar dasu ciki har da ma’aikatar harkokin kasashen wajen Amurka, suna hasashen yan gudun hijira zasu kai dubu 85 da zasu iso kafin karshen wannan wata.
A yayin da Turai take kokarin amsar dubban daruruwar yan gudun hijira da masu neman mafaka a shekarar 2015, gwamnatin Obama ta bada sanarwar Karin adadin ‘yan gudun hijira da Amurka ta basu matsugunai a wannan shekarar kudi zasu kai daga dubu 70 zuwa dubu 85. Wannan matakin da ya hada da karban yan gudun hijira daga Syria dubu 10, ya dora babban nawaya a kan kungiyoyin cikin gida da zasu taimakawa sabbin zuwar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG