Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Amince Da Sayar wa Najeriya Jiragen Yakin Zamani


 A-29 Super Tucano
A-29 Super Tucano

Amurka ta amince za ta sayarwa Najeriya manyan jiragen yakin nan samfurin A29 Super Tucano guda 12, don gamawa da sauran burbushin Boko Haram.

Nan bada dadewa ba ake sa ran gwamnatin shugaba Donald Trump za ta sanarwa da Majalisar Dokoki a hukumance kudurin Amurka na sayarwa Najeriya manyan jiragen yakin nan da ake yayi A29 Super Tucano.

A baya dai Amurka ta yi ta sa tarnaki wajen sayarwa Najeriya makamai bisa zargin dakarun ‘kasar na take hakkin bil Adama, a dai dai lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram ke rawar gaban hantsi.

Shi dai wannan sabon jirgin na A29 Super Tucano da ake yayi ya banbanta da wanda yanzu haka dakarun Najeriya ke amfani da shi, kasancewar zai iya hango makiya daga nesa ya kuma kai musu hari ko dare ko rana, haka kuma manyan bindigogin nan na kakkabo jiragen sama basa iya tasiri a kansa.

Wannan mataki dai na gwamnatin Donald Trump ya zo da mamaki ga mafi yawan ‘yan Najeriya, sai dai gogaggen jami’in diplomasiya Ambasada Sulaiman Dahiru, yace bai yi mamaki ba kasancewar ‘yan jam’iyyar Democratic Party sun fi bayar da muhimmanci kan wannan batu, amma ‘yan jam’iyyar Republican basu cika damuwa game da irin wadannan abubuwa ba.

Gwamnatin Najeriya dai ba ta nemi wannan bukata daga gwamnatin Amurka ba, tun lokacin shugaba Goodluck Jonathan aka nemi wannan bukata yayin da Amurka ta sa ‘kafa ta shure a wancan lokacin.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

DOMIN KARIN BAYANI

Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci http://bit.ly/2kT7h6n

Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci http://bit.ly/2lujeAU

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG