Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ba Da Tabbacin Tura Jiragen Ruwanta Zuwa Tekun Pacific


Jirgin yakin Amurka na USS Carl Vinson
Jirgin yakin Amurka na USS Carl Vinson

Amurka ta tabbatarwa da kawayenta cewa ayarin jiragen yakin ruwa na USS Carl Vinson ya kama  hanyarsa ta zuwa arewacin tekun Pacific don takawa shirin nukiliyar Korea ta arewa burki.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da aka sami rahotanni masu karo da junan suna cewa jirgin ruwan mai dakon jirgen sama da ma wasu jiragen ruwa sun riga sun tafi yankin tekun na pacific.

Da ya ke magana ranar 11 ga watan nan na Afirilu, shugaba Donald Trump ya ce "za mu tura ayarin jiragen ruwa" wato Armada a turance, kwanaki uku bayan da gungun jiragen yakin suka bar yankin Singapore.

Admiral Harry, kwamandan rundunar sojan ruwan Amurka a yankin Pacific, ya sanar cewa ranar 9 ga watan nan cewa ya ba da umurnin jiragen yakin su nufi arewa, bayan sun bar Singapore kuma ba za su tsaya gabar Australia ba kamar yadda a da suka tsara.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG