Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ci Gaba Da Kasancewa Kasa Ta Farko A Fannin Sayar Da Makamai A Duniya


Makamai
Makamai

Wani rahoto ya nuna cewa, Amurka na cigaba da zama kasar da ta fi kowace sayar da makamai a duniya, inda ta samu kusan dala biliyan 23 daga makaman da ta sayarwa kasashe a shekarar da ta gabata, musamman kasashen da ke Gabas ta Tsakiya.

Rahoton wanda ya fito daga wani kamfani da ke bibiyan hadahadar makaman kariya a duniya, ya nuna cewa an samu karuwar cinikayyar makamai a kasuwar duniya daga dala biliyan 6.6 a bara zuwa dala biliyan 65.

A Amurka adadin kudin ya kai dala biliyan 23 a bara, ya kuma karu da dala biliyan 10 tun bayan rahoton da aka fitar a shekarar 2009.

Fannin sayar da makaman kariya na duniya bai taba ganin irin wannan tashin kudin cinikayya ba kamar yadda aka gani a shekarar 2014 da kuma 2015 a cewar Ben Moores, wani mai fashin baki a kamfanin na IHS.

Itama Faransa cinikin sayar da makamanta ya rubanya a shekara ta 2015.

Idan aka kwatanta da shekarar 2014, inda ya tashi daga dala biliyan takwas zuwa dala biliyan 18.

A cewar rahoton, idan har kuma aka tafi akan wannan turba, nan da shekarar 2018, Faransa za ta dare kasar Rasha wacce ita ce kasa ta biyu a sayar da makamai a duniya.

Wannan kari na sayar da makamai da aka gani, na da nasaba da yawan makaman da ake bukata daga Gabas ta Tsakiya, yankin da ya fi kowane bukatar kayan kariya.

Kuma yankin shi ne a gaba-gaba a masu sayen makamai, inda akan kashe biliyan 21.6 wajen sayen makaman, ciki har da dala biliyan 8.8 daga Amurka.

XS
SM
MD
LG