Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Daina Sayen Man Najeriya


Shugaba Goodluck Jonathan da Shugaban Amurka Barack Obama.
Shugaba Goodluck Jonathan da Shugaban Amurka Barack Obama.

Najeriya ta sanarda dakatar da shirin horas da dakarunta da tayi da Amurka sabili da wasu dalilai da bata bayyana ba. To amma Muryar Amurka tayi firar da wani masani akan harkokin tsaro.

Dr. Abdullahi Wase masani akan harkokin tsaro yace kafin sanarwar da Najeriya ta fitar Amurka ta riga ta dakatar da sayen man Najeriya.

Bayan Amurka ta hana sayen man Najeriya bata tsaya nan ba. Ta hana sayarwa gwamnatin Najeriya makamai hatta harsashi kuma ta umurni kasashen Faransa da Birtaniya su yi hakan.

Amurka ta dauki matakan ne domin tana ganin gwamnatin Najeriya nada sakaci akan tabarbarewar tsaro a kasar. Tana ma tunanen gwamnatin Najeriya din tana marawa tashin tashinar kasar baya. Amurka tayi kokari ta ja kunnen gwamnati amma taki ta ji. Tsohon jakadan Amurka kafin ya tashi yace dole kasar ta dauki wasu matakai idan kuma ta ki to kafin shekarar 2015 za'a samu mummunan sakamako. Yace idan ba'a son kasar ta wargaje to dole ne gwamnati tayi takastantsan.

Rashin ganin gwamnatin Najeriya tayi takatsantsan ya sa Amurka ta hana sayarwa kasar makamai da kuma daina sayen man Najeriya. Ban da haka Amurka tayi korafin cewa bata ga alamar za'a bari ta koyas da sojojin Najeriya yadda yakamata ba. Tun kafin sanarwar dakatar da shirin Amurka tayi watsi dashi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG