Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gamsu da Salo da Tsarin Mulkin Shugaba Buhari


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Gwamnatin Amurka ta nuna gamsuwarta da tsare tsaren gwamnatin Shugaba Buhari musamman a bangaren yaki da ta'addanci da cin hanci da rashawa

Mukaddashin darakta a ma'aikatar harkokin wajen Amurka Mr. Nathan Holt shi ya bayyana hakan a wata muamala da aka yi tsakanin hukumomin Amurka da na Najeriya.

Mr. Holt yace Amurka ta gamsu kuma tayi na'am da irin matakan da Najeriya ke dauki wurin farfadowa da tattalin arziki da kokarin samar da aikin yi da yaki da ta'addanci da kuma yaki da ayyukan zarmiya. Yace Najeriya ta shiga jerin kasashen duniya dake bin tsare tsare na kasa da kasa da aka amince dasu akan gudanar da mulki.

Akan wannan ne Muryar Amurka tayi fira da Ministan Tsaron Najeriya Mansu Dan Ali domin jin yadda suka dauki rahoton da kuma irin matakan da zasu dauka nan gaba.

Inji Janar Mansur Dan Ali ba Amurka kadai ba duk inda suka je ana yaba masu. Yace irin wadannan yabon ba zai sa su kauce daga abubuwan da su keyi ba a matsayinsu na kasancewa gwamnati.

Abubuwan da suka kawowa kasar karramawa sun hada da ceto fiye da kashi hamsin na 'yan matan Chibok da aka sace. Rugurguza Boko Haram wani abun yabawa ne. Dangane da yaki da cin hanci da rashawa kullum ake yin kamu kuma kasashen waje suna yabawa

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG