Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Koriya Ta Arewa Kan Sakamakon Nutsar Da Jirgin Koriya Ta Kudu


Garwar jirgin ruwan yakin Koriya ta Kudu mai suna Cheonan
Garwar jirgin ruwan yakin Koriya ta Kudu mai suna Cheonan

Amurka ta ja kunnen Koriya ta Arewa cewar zata ga sakamakon nutsar da jirgin ruwan Koriya ta Kudu da ta yi, tana mai bayyana lamarin a zaman mummunar tsokana.

Amurka ta gargadi Koriya ta Arewa cewa za ta ga sakamakon nutsar da jirgin ruwan yaki na Koriya ta Kudu da ta yi.

Wannan kashedin ya fito daga bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, P.J. Crowley, wanda ya fadawa 'yan jarida cewa abinda Koriya ta Arewa ta yi "mummunar tsokana" ce kuma ba za a yarda da hakan ba.

Amma manyan jami'an Amurka sun guje wa bayyana wannan harin a zaman ayyana yaki, ko kuma ta'addanci na gwamnatin wata kasa. Manyan jami'an soja na Amurka sun ce ya rage ma Koriya ta Kudu ta san irin matakin da za ta dauka kan wannan abu.

Wata kungiyar masu bincike na kasa da kasa ta fito jiya alhamis tana zargin Koriya ta Arewa da laifin nutsar da wannan jirgin ruwan yaki na Koriya ta Kudu a cikin watan Maris.

Koriya ta Arewa ta yi fatali da sakamakon binciken kungiyar, tana mai bayyana rahoton a zaman "kage" kuma "maras tushe." Hukumar Tsaron Kasa ta Koriya ta Arewa ta yi barazanar cewa kasar zata kaddamar da yaki gadan-gadan a kan duk wani matakin da za a dauka na mayar da martani game da nutsewar jirgin.

Rahoton kungiyar da ta yi binciken ya ce wani jirgin karkashin ruwa na Koriya ta Arewa ne ya harba wani makami mai linzami na karkashin ruwa a kan jirgin ruwan yaki na Koriya ta Kudu mai suna Cheonan a watan Maris, ya haddasa mummunar fashewa karkashin ruwa har wannan jirgi ya rabe gida biyu.

Shugaba Lee Myung-bak na Koriya ta Kudu ya ce hukumomi a birnin Seoul za su dauki abinda ya kira, "matakan mayar da martani masu tsanani." Bai yi karin bayani kan wannan ba.

XS
SM
MD
LG