Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi ‘Yan Kasar Dake Zaune A Kasar Kenya


Amurka ta gargadi ‘yan kasar dake zaune a kasar Kenya, ko suke da niyyar zuwa kasar da suyi hattara, domin yiyuwar barkewar tarzoma sakamakon zaben da za ayi a kasar ranar 8 ga watan Agusta.

A cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin waje ta fitar jiya alhamis tace gangami da zanga-zanga da ake niyyar yi na lumana na iya rikidewa ya zame na tashin hankali.

Sanarwar taci gaba da cewa masu aikata ayyukan assha da ‘yan ta’adda na iya labewa da wannan zanga-zangar domin cimma burin su, musamman ga baki.

Tun da farko dai madugun ‘yan adawa Raila Odinga, yayi gargaddin cewa za a gudanar da gagarumin gangami muddin aka nemi ayi magudi a zaben.

Dama dai kasar ta Kenya, tana da tarihin tashin hankalin zabe, a shekarar 2007 mutane sama da 1,200 ne aka kashe bayan zanga-zangar bayan zabe, wanda kuma fadan ya rikide ya koma na kabilanci, To sai dai zaben shekarar 2013 anyi shi cikin lumana

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG