Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta gayyaci Farfasa Jega zuwa kasar Nijar


Farfasa Attahiru Jega thoshon shugaban hukumar zaben Najeriya INEC
Farfasa Attahiru Jega thoshon shugaban hukumar zaben Najeriya INEC

Gwamnatin Amurka ta gayyaci Farfasa Attahiru Jega tshohon shugaban hukumar zaben Najeriya wato INEC domin ya taimakawa hukumar zaben Nijar CENI ta warware tsalolin da take fuskanta

Ofishin jakadancin Amurka dake Nijar ne ya gayyaci Farfasa Attahiru Jega zuwa kasar domin taimakawa hukumar zaben Nijar din wato CENI ta magance matsalar da take fuskanta.

Farfasa Jega zai karawa CENI dabarun tsara zabe yadda zai zama da inganci da adalci yayinda take shirin tsara zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Farfasa Jega yace sun yi anfani da damar da karawa juna ilimi. Ya bada kasida ga ma'aikatan CENI tare da ziyartar duk manya manyan 'yan siyasa da suke da rawar da zasu taka a zaben. Ya ziyarci hukumar dake kokarin kawo daidaituwa tsakanin 'yan siyasa wato CNDP. Ya sadu da wakilan hadakar jam'iyyun siyasa dake adawa da ake kira COPA. Haka ma ya gana da wakilan kungiyoyin dake goyon bayan jam'iyyar dake mulki yanzu.

Dangane da koke-koken 'yan adawa yace a yi kokari a tattauna domin a samu masalaha a kuma yi tafiya tare. Kowane zabe akan samu kace na ce amma 'yan siyasa suna da haki su tattauna a samu masalaha domin kasa ta cigaba.

Shugabannin hukumar zaben Nijar CENI sun bayyana gamsuwa da gudummawar Farfasa Jega kuma a cewar mataimakiyar shugaban CENI Hajiya Maryama Katambe akwai abu da yawa da suka karu dasu har da litattafai da ya basu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG