Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Juya Kan Iran Da Hezbollah


Mayakan Hezbollah
Mayakan Hezbollah

A jiya Alhamis Jakadiyar Amurka a majalisar Dinkin Duniya ta juya kan Iran da ‘yan kanzaginta Hezbollah, tana cewar Amurka zata dau matakin dakile, abin da ta kira, “wadannan masihun da ke ta ‘kara ta’azzara.”

A wani zaman kwamitin sulhun majalisar Dinkin Duniya na kowani wata a kan batutuwan da suka shafi Gabas ta Tsakiya, musamman batun Isra’ila da Falasdinawa, Nikki Haley ta ce kwamitin ya Fadada tattaunawar ta yadda ta hada da sauran abubuwan dake yin barazana ga yankin.


Ta ce “Yakamata mu fara da manyan masu laifi, Iran da mukarrabanta mayakan Hezbollah,” wato kungiyar ‘yan bindigar Shi’a dake Lebanon da Amurka ta ayyanasu kungiyar ta’addanci.

Tace wadannan kawaye biyu suna haddasa rashin zaman lafiya a yankin ta hanyar shirya ta’addanci da ayyukan soji.

Wadannan kawaye suna taimakawa Bashar al-Assad a kisan dubban fararen hula da yake yi, wanda ya jefa miliyoyin yan gudun hijira cikin mawuyacin hali, inji jakadiya Haley a lokacin da take nuni da rawar da Iran da Hezbollah ke takawa a yakin kasar Syria.


A yayid da wannan kwamiti bai bada muhimmanci ga wannan lamari, ta yi kashedin cewar Amurka zata maida hankali a wurin.

Tace zasu yi magana a kan Iran da Hezbollah tare da daukar mataki a kan rashin da’a da suke aikatawa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG