Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Kashe Dala Biliyan $3.6 Domin Yakin Cutar Kanjamau a Shekaru 10


Ambasadon Amurka a Nijeriya, James Entwistle
Ambasadon Amurka a Nijeriya, James Entwistle

Ambasadon Amurka a Nijeriya, Mr. James Entwistle, yace gwamnatin tarayyar Amurka ta kashe fiye da dala $3.6 a yaki kan cutar kanjamau a kasar Nijeriya cikin shekaru 10.

Ambasadon Amurka a Nijeriya, Mr. James Entwistle, yace gwamnatin tarayyar Amurka ta kashe fiye da dala $3.6 a yaki kan cutar kanjamau a kasar Nijeriya cikin shekaru 10.

Entwistle ya fadi haka ne a yayin wani tattaunawa da ‘yan jaridu a jihar Sokoto. Inji shi, wannan yawan kudin da aka kashe a shekarun da suka wuce wata alama ce ta mika kan gwamnatin Amurka ta yaki da wannan damuwar a cikin kasar.

Ya nuna cewa Amurka tana da hadin hannu da NACA, da sauran kungiyoyi masu bada taimako a Nijeriya domin kokarin kauda wannan bakin yanayin.

Yace, "Muna aiki tare da NACA da sauran kungiyoyi domin yaki da cutar kanjamau, da kokarin yaki da wannan bakin yanayi da ya dami jama’a da yawa.” Ambasadon ya lura da cewa, ko da yake cutar kanjamau na da wahalar warkarwa, an sami cigaba sosai a kokarin kauda wannan cutar a kasar.

Entwistle ya lura cewa kasashe da yawa a Afrika sun wuce Nijeriya wajen yaki da cutar kanjamau. Ya kuma baiyyana cewa akwai bukatar hukumomi su kara kokari domin su kauda wannan cutar daga Nijeriya.

Yace kasar na cin nasara a yakinta kan cutar kanjamau, musamman da shigowar kungiyoyin bayar da taimako, wadanda ke aiki sosai domin fadakar da jama’a akan illar da wannan cutar ke kawowa.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG