Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta maida martanin soja kan barazanar da Rasha ke yi


A U.S. Navy F-18 fighter jet takes off from the deck of the USS Carl Vinson (CVN 70) aircraft carrier following a routine patrol off the disputed South China Sea, March 3, 2017.
A U.S. Navy F-18 fighter jet takes off from the deck of the USS Carl Vinson (CVN 70) aircraft carrier following a routine patrol off the disputed South China Sea, March 3, 2017.

Kakakin fadar White House ya shaidawa manema labarai jiya Litinin cewa, “Zamu yi dukan abinda muka iya wajen kare muradunmu, yayinda yake kare shawarar da aka yanke ta harbo jirgin saman Syria SU-22 da ya kaiwa dakarun hadin guiwa hari a kusa da garin Tabqan na Syria.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya bayyana harbo jirgin a matsayin takala. Sanarwar da ministan ya fitar a birnin Moscow tayi gargadi da cewa, za a dauki jiragen dakarun hadin guiwar a matsayin abokan gaba, ya kuma ce za a toshe hanyar tuntubar da zata sa a kauracewa karo a aikin soji cikin kuskure.

Spicer ya fada jiya Litinin cewa, Washington zata bar kofar tuntuba a bude domin warware wadansu matsaloli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG