Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tallafawa Kasar Habasha Da Dala Miliyan 97


Ethiopia African Union Summit
Ethiopia African Union Summit

Hukumar bada tallafi ta Amurka ta sanar da bada tallafin makudan kudin agajin da suka kai Dala Miliyan 97 a matsayin daukin gaggawa ga kasar Ethiopia na matsalar masifar da kan shafi bil’adama da suke fuskanta na dumamar tekun da ake cewa El’Nino.

“Shugabar na USAID wato Gayle Smith yace, “Amurka na taimakawa ‘yan kasar ta Habasha ne saboda su rage radadin wannan matsala ta yanayin dumamar teku da ke haifar da matsaloli a nahiyar game da abinci da makamantansu”.

Ta sanar da haka ne a wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta ci gaba da bayyana yadda wannan dumamar tekun ta shafi amfanin gonar da hakan ya kawo karancin abinci da kara tsadar rayuwar yau da kullum ga talakawa.

Cikin taimakon har da abincin da ya kai Ton 176,000 da za a rabawa jama’a.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG