Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Sudan Sabo Da Matakan Murkushe Masu Zanga Zanga.


Wata maajiyar mai a Sudan
Wata maajiyar mai a Sudan

Da kakkausan harshe jami’an Gwamnatin Amurka suka la’anci matakan da hukumomin kasar Sudan suka dauka na amfani da karfi kan masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Sudan.

Da kakkausan harshe jami’an Gwamnatin Amurka suka la’anci matakan da hukumomin kasar Sudan suka dauka na amfani da karfi kan masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Sudan da aka rika yi a sassa daban-daban na kasar.

Masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Sudan sun farota ne tun daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan makonni biyun da suka gabata, lokacin da dalibai suka fara haduwa domin daga muryar nuna kyamarsu ga sabon shirin Gwamnatin Sudan kan tsuke bakin aljihun da yanzu ya janyo hauhawar farashin kaya.

Zanga-zangar sai ta sami karbuwa a sassa daban-dabam na biranen kasar Sudaan, har ta fara akazancewa a birnin Khartoum. Ba tare da bata lokaci ba sai jami’an tsaron Gwamnatin Sudan suka maida martani ta amfani da kulake suna dukan masu zanga-zanga tare da harba hayaki mai sa hawaye, su kuma masu zanga-zangar suka rika jifan jami’an tsaron da duwatsu, suna kuma kokkona tayioyi a kan tituna.

Jami’ar dake Magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland jiya Talata tace daga irin rahotannin da ake samu jami’an tsaron Gwamnatin Sudan suna kama masu zanga-zangar suna turawa Kurkuku ba tare da gurfanar dasu gaban shari’a ba. Jami’ar ta Amurka tayi gargadin cewar ba za’a iya maganta matsalar tattalin arzikin kasar Sudan ta hanyar cin mutuncin ‘yan kasar Sudan ba, don haka tayi kira ga Gwamnatin Sudan da a gaggauta sakin wadanda ake tsare dasu a dalilin yin zanga-zanga.

XS
SM
MD
LG