Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Rokon Ayi Zaben Gaskiya Cikin Lumana A Senegal


Shugaba Abdoulaye Wade, yana kyamfe ran laraba, 22 Fabrairu 2012, a Dakar, babban birnin Senegal.
Shugaba Abdoulaye Wade, yana kyamfe ran laraba, 22 Fabrairu 2012, a Dakar, babban birnin Senegal.

Kakakin shugaba Obama ya roki jami'an zabe da su tabbatar da cewa kuri'ar da jama'a suka jefa ita za a yi aiki da ita.

Amurka ta yi kira ga hukumomin kasar Senegal da su tabbatar da cewa an gudanar da zaben shugaban kasa na ranar lahadi mai zuwa cikin lumana, tsakani da Allah ba tare da ha’inci ba.

Sakataren yada labarai na shugaba Barack Obama ya bayarda sanarwa a yau alhamis yana yin kira ga jami’an zabe na Senegal da su tabbatar da cewa kuri’ar da jama’a zasu jefa ita za a yi amfani da ita.

Sanarwar ta yi kira ga masu jefa kuri’a a Snegal da su yi wannan zabe cikin lumana, tare da yin kira ga dukkan bangarorin kasar, ciki har da jami’an tsaro kan su guji tayar da fitina ko zub da jini.

Masu zanga-zanga sun yi arangama da ‘yan sanda sau da dama cikin wannan wata a Dakar, babban birnin kasar, a yayin da suke kokarin yin gangamin nuna rashin yarda da kokarin shugaba Abdoulaye Wade na yin tazarce a kan mulki.

Shugaban mai shekaru 85 da haihuwa yana takara a karo na uku, duk da cewa tsarin mulkin kasar yace wa’adi biyu kadai shugaba zai yi a kan mulki. Kotun koli ta Senegal ta yanke hukumcin cewa wannan tanadi bai shafi Mr. Wade ba tun da an riga an zabe shi kafin a fara yin aiki da tanadin.

XS
SM
MD
LG