Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta yi Tir da Hare-haren da Boko Haram ke Kaiwa


Motar da Boko Haram ta kona
Motar da Boko Haram ta kona

Amurka ta yi Allah wadai da munanan hare-haren da ake zargin Kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lid-Daawati wal Jihad

Amurka ta yi Allah wadai da munanan hare-haren da ake zargin Kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lid-Daawati wal Jihad, wadda ake wa lakabi da Boko Haram, ta kai ranar Lahadi, a jihohin Borno da Adamawa dake Nijeriya, da suka yi sanadin mutuwar dinbin fararen hulan da basu ji ba basu gani ba.

A ta bakin Amurka, "Mu na goyon bayan hukumomin Nijeriya a yayin da suka fara bincike game da wadannan hare-haren, kuma muna kira ga 'yan kasar su goyi bayan wannan kokari ta hukumomin kasar na ganin an gurfanar da wadanda su ka aikata wadannan laifuka a gaban shari'a."

Amurka dai na cigaba da goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya a fafatukar da suke yi na dakile tsattsauran ra'ayi mai haddasa tashin hankali, da kuma taimaka wa gwamnatin Nijeriya a kokarinta na yin fito-na-fito da barazanar da kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lid-Daawati wal Jihad da sauran kungiyoyi masu alaka da ita.
XS
SM
MD
LG