Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na Zargin Rasha da Zanga-zanga a Gabashin Ukraine


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Bayan da Rasha ta hada yankin Cremia da kasarta sai gashi kuma wasu Rashawa sun tayarda karin baya a gabashin Ukraine lamarin da Amurka tace ta haddasa sabon rikicin.

Fadar shugaban Amirka ta White House tace tana da kwakwarar shedar cewa wasu masu zanga zangar goyon bayan Rasha da suka mamaye gine ginen gwamnati a biranen gabashin kasar Ukraine a ranar Lahadi, ba mazauna yankunan bane, wasu mutane ne da aka biya domin suyi wannan zanga zangar.

Jiya Litinin wani mai magana da yawun fadar shugaban Amirka ya fadawa 'yan jarida cewa gwamnatin Obama ta bukaci kasar Rasha data daina yin shishigi a gabashin kasar Ukraine, kuma tayi barazanar cewa idan Rasha tayi kunen kashi ga wannan bukata, to zata aza mata karin takunkunmi.

Shima sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, a jiya Litinin ya zanta da takwaran aikinsa na Rasha Sergei Lavrov, a tattaunawar baya bayan nan daga cikin shawarwarin da suke yi akan al'amari kasar Ukraine.

John Kerry ya bukaci Rasha data fito filli tayi Allah wadai da aiyukan masu neman balewa a zaman masu yin zagon kasa da kuma tsokanar fada.

Ma'aikatar tsaron Amirka da ake cewa Pentagon ta tabbatar cewa jiragen ruwan yakin Amirka sun doshi tekun Bahar Asuwad domin marawa kawayenta na turai da suke yankin
XS
SM
MD
LG