Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Kara Tura Sojoji 560 Kasar Iraqi


Amurka za ta tura karin sojoji 560 zuwa Iraki don su taimaka a yakin sake kwato birnin Mosul daga hannun ISIS, bayan sake kwato wani muhimmin filin saukar jiragen yaki, wanda ke daura da birnin da sojojin Iraki su ka yi.

Sakataren Tsaro Ash Carter ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar da ya kai birnin Bagadaza ranar Litini. Ya ce za a tura karin sojojin ne su ba da kariya ga karamin filin jirgin saman Qayyarah, mai tazakar kilomita 60 kudu da birnin na Mosul, wanda za a yi aiki da shi a matsayin wurin sauka da tashi, ko kuma yada zango, ga jiragen yakin sojojin gamayya.

Janar Sean Macfarland, kwamandan sojojin gamayya a Iraki, ya gaya ma manema labarai jiya Litini a birnin Bagadaza cewa wani rukuni na sojojin za su zauna ne a Qayyarah, yayin da wasunsu kuma za su rika kai kayayyaki zuwa wannan karamin filin jirgin saman daga wasu wuraren.

Kwace karamin filin jirgin saman da sojojin Iraki su ka yi, shi ne cikamakon matakai 10 na zangon farko na shirin sojojin gamayyar na gamawa da ISIS, a cewar wani babban jami'in Ma'aikatar Tsaron AMurka. "Hakika Qayyarah wani babban kamu ne bisa ga tsarin saboda matukar amfaninsa," a cewar babban jami'in, wanda ya bukaci a sakaya sunansa.

A karo na hudu na ziyararsa zuwa Iraki a matsayin Sakataren Tsaro, Carter ya gana da Firaministan Iraki Haider al-Abadi da kuma Ministan Tsaro Khalid al-Obeidi a birnin Bagdza, zai kuma yi magana ta waya da Masoud Barzani, Shugaban Kurdawan Iraki. Carter ya ce Abadi ya jaddada masa a ganawar tasu cewa ya na so ida farmaki kan Mosul din a wannan shekarar.

XS
SM
MD
LG